Home Global Hukumar Alhazai ta Ghana ta sanar da dalar Amurka dubu 6,500 a matsayin kudin aikin Hajjin bana
Global - March 4, 2023

Hukumar Alhazai ta Ghana ta sanar da dalar Amurka dubu 6,500 a matsayin kudin aikin Hajjin bana

 

Hukumar Alhazai ta Ghana ta sanar da cewa dalar Amurka dubu 6,500,  kwatankwacin Ghana Cedi 75,000 a matsayin kudin aikin hajjin shekarar 2023.

Wata wasika mai dauke da kwanan wata 1 ga watan Maris, da kuma sa hannun shugaban hukumar, Hon. Ben Abdallah Banda da babban sakataren hukumar Alh Faroul Hamza ta ce “Hukumar Hajji ta Ghana na son sanar da masu son zuwa aikin hajjin bana cewa za a  biya kudin aikin hajjin bana a kan dala dubu 6,500 wanda ke daidai GHC 75,000.

Hukumar ta sanya ranar 30 ga watan Afrilu a matsayin wa’adin biyan kudin.

 

About Post Author

Check Also

Hajj 2023: Malaysia TH to give financial aid to First-time pilgrims

  Lembaga Tabung Haji (TH) has allocated more than RM400 million towards subsidising …